Labaran Kano
Za mu magance cunkoso a makarantu-KSSSMB
Hukumar da ke kula da manyan makarantun sakandire ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf domin magance matsalar samun cunkoso a ajujuwan da ke makarantun jihar ta hanyar gina bennayi da zasu samar da sababbin ajujuwa ga dalibai.
Babban sakatare a hukumar Dr Bello Shehu ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio da ya mayar da hankali kan magance matsalolin manyan makarantun sakadiren kasar nan.
Ya kara da cewa, a kullum hukumar na gudanar da kewaye a makarantun sakandire wanda hakan ne ya basu damar gano malamai masu aikata laifukan da suka shafi tauye hakkin koyarwa kuma za su dauki matakin da ya dace akansu.
Sai dai ya ce hukumar ta shirya domin baiwa malamai damar zuwa karo karatu matukar abinda malamin zai koyo yana kan fanni da yake koyarwa a wani mataki na samar da ingantaccen karatu ga dalibai.
Dr Bello Shehu ya kuma ja hankalin shugabannin makarantu da su kiyaye bayar da damar yin amfani da makarantun matukar ba sha’anin da ya shafi harkar koyo da koyarwa ba.