Ƙetare
Za mu taimaka wa Najeriya wajen yaki da rashin tsaro a Arewacin kasar – Emmanuel Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa za ta taimaka wa Najeriya domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar arewacin ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X, shugaba Macron ya ce ya nemi sauran ƙasashe ƙawayensu da su “ƙara ƙaimi a hulɗarsu” da Najeriya.
“Na yi magana da Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shaida masa goyon bayan Faransa game da matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya,” a cewar Macron.
Kalaman Macron na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke zargin gwamnatin Najeriya da ƙyale ‘yanbindiga suna yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla, iƙirarin da gwamnatin Tinubu ta musanta.
You must be logged in to post a comment Login