ilimi
Za mu tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani – ASUP
Kungiyar Malaman Makarantun Kwalejin Ilimin Kimiyya da Fasaha ASUP, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.
Kungiyar ta ce daga ranar 6 ga watan Afrilu zata shiga yajin aikin kan abin da ta kira rashin cika alkawari da gwamnatin tarayya ta yiwa wasu jihohi.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar bayan taron majalisar zartarwa ta kasa a yau Juma’a.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabanta Mista Anderson Ezeibe, ta ce sun yanke shawarar ne domin su ja hankalin gwamnati kan bukatar biyan su kudaden su na tsawon watanni 10 da ta ke bi bashi da kuma batun mafi karancin albashi ga malaman makarantun kimiyya da fasaha na tarayya.
Kungiyar ta kuma bukaci wasu gwamnatocin jihohi da su biya bashin da ke kan ta musamman na jihohin Abia, Ogun, Osun, Benue, sai Plateau da Edo.
Sauran su ne CrossRiver Sokoto Kaduna, da Adamawa da dai sauransu.
You must be logged in to post a comment Login