Labarai
Za mu yi ƙoƙarin ganin an sanya sarakunan gargajiya cikin sha’anin tsaro – Wazirin Dutse
Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan Arewa (ACF) Alhaji Bashir Ɗalhatu Wazirn Dutse, ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya baiwa sarakunan gargajiya damar shiga sha’anin tsaro.
A cewar sa, akwai buƙatar a samar da doka wadda za ta baiwa sarakunan gargajiya damar bada gudunmawa wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi yankin Arewacin Najeriya.
Alhaji Bashir Ɗalhatu ya yi wannan kira ne, yayin walimar taya shi murnar zama shugaban kwamitin amintattu da ƙungiyar ACF ta naɗa shi.
“Muna kira ga dukkanin shugabannin rundunonin tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya, duk da mun san suna iya bakin ƙoƙarinsu” a cewar Alhaji Bashir Ɗalhatu.
Ya kuma ce “Sanin kowa ne a shekarun baya babu wani baƙo da zai shigo gari ba tare da sanin mai unguwa ba, don haka muna son wannan tsarin ya dawo a wannan lokacin.
Haka kuma ya tabbatar da cewa, wannan matsayi da ya samu zai yi amfani da shi wajen farfaɗo da martabar dattawa, domin suna sane da ƙorafin al’umma da suke zargin cewa babu dattijantaka a Najeriya.
Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ƙara da cewar, zai yi waiwaye kan wasu batutuwa don samar da gyara, yana mai cewa akwai fahimtar juna tsakaninsa da shugaban ƙungiyar ta ACF tun a makaranta har zuwa yanzu.
Da yake batu kan yunƙurin wasu ɓangare na al’ummar ƙasar nan kan iƙirarinsu na a raba ƙasar, Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ce “Masu iƙirarin raba Najeriya ba za su samu nasara ba, domin muna da yaƙinin ko ƙudirinsu ya yi nasara to ba za su samu nasarar ba, mu ne da nasara, domin mune muke da al’adun gargajiya tun iyaye da kakanni”.
A ƙarshe Alhaji Bashir Ɗalhatu ya tabbatar da cewa, zai yi aiki ba dare ba rana kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi yankin Arewacin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login