Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Buhari ya shigo da masu rike da sarautun gargajiya wajen inganta tsaro-Sarkin Alkalman Kano

Published

on

An  shawarci gwamnatin shugaba   Muhammadu Buhari,  da ta  shigo da  masu rike da mukaman gargajiya da sarakunan musulunci wajen magance matsalar tsaro data dabaibaye kasar nan.

Sarkin Alkalman Kano Alhaji Ilyasu Labaran Daneji, ne  ya bayyana hakan ga manema labarai a zantawa ta musamman da ya yi dasu danagen da matsalolin tsaro da kasar ke fama dashi.

Sarkin Alkalman,  ya  ce a shekarun da suka shudea baya irin wannan tsarin aake dashi  a kauyuka da birane , wanda a halin yanzu anyi watsi da tsarin , duba da haka akwai bukatar dawo da tsarin  don  magance matsalar tsaro musamman da tafi addabar  yankin Arewacin kasar nan.

Labarai masu alaka.

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro

Rundunar Sojin Najeriya za ta hada kai da Mafarauta da yan Vigilante don inganta tsaro

Alhaji Ilyasu Labaran Daneji ya kara dacewa hakan zai taimaka kwarai wajen inganta tsaro  kasancewar masu rike da mukamai na gargajiya da sarakunan musulunci sun fi kusanci da  talakawa don haka su zasu fi sanin matsalolin dake addabar su akan lokaci.

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa, wakilin mu da ya halarci taron  ya ruwaito cewar  Sarkin Alkalman Kano, ya yi kira da al’ummar kasar nan da su  addu’oin dqa kuma daukan matakan kare kai daga  cutar nan ta Corona virus ami lakabin  Covid-19 , duba da yadda da cutar ke cigaba da yaduwa  a kasashen duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!