Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu yi aiki kafada da kafada da kowacce Kabila a Kano – CP Dikko

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Samaila Shuaibu Dikko ya tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da adalci ba tare sun nuna kabilanci ba.

Samaila Shuaibu ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Yarbawa da Igbo mazauna Kano don taya shi murnar kama aiki.

A cewar sa ayyukan rundunar ba zasu tafi yadda ya kamataba ba, har sai an samu hadin kai daga al’umma wajen magance matsalolin da suke damun su.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Yarabawa mazauna Kano injiniya Murtala Alimi ya ce, sun kai ziyarar ne don nuna goyon bayan da kuma tabbatar da cewa za su bada hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya.

Haka zalika shima shugaban kungiyar Kabilar Igbo mazauna Kano Dr. Boniface Igbekwr cewa yayi Kano na daya daga cikin jihohin da suka fi ko’ina zaman lafiya a don haka zasu bai wa rundunar hadin kai wajen gudanar da duk ayyukansu.

Kwamishinan Yan sandan ya ya gana da kungiyoyin matuka baburan adaidaita sahu na Kano inda ya tabbatar musu da cewa su shaidawa mambobin kungiyarsu cewa kofar rundunar a bude take wajen gudanar da ayyukansu tare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!