Labarai
Za mu yi haɗin gwiwa da Gwamnatin Kano don bunƙasa kirkire-kirkire da makamashi- Gwamnatin tarayya

Ministan Kirkire-Kirkire da Kimiyya da Fasaha Uche Nnaji, ya bayyana cewa ma’aikatarsa za ta yi haɗin gwiwa da Gwamnatin jihar Kano domin bunƙasa kirkire-kirkire da harkokin makamashi.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a baya-bayan nan, inda ta bayyana ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin Kwamishinan ma’aikatar Kirkire-kirkire, da Kimiyya da Fasaha na Kano Dakta Yusuf Kofar Mata, a ofishinsa da ke Abuja.
A cewar sanarwar, ministan ya bayyana jihar Kano a matsayin “jihar da ta fi kowacce muhimmanci a tsarin sauyin ci gaba na gwamnatin tarayya ta fuskar kirkire-kirkire.”
Ministan ya kuma yaba da yadda jihar Kano ke aiwatar da shirye-shiryen kirkire-kirkire kamar yadda Dakta Yusuf Kofar Mata ya sanar da shi.
Daga cikin waɗannan shirye-shirye akwai shirin wayar da kan matasa da masu sana’o’i a fannin fasahar zamani, da kuma sauya makarantun sakandire guda 44 zuwa cibiyoyin koyon sana’o’i da fasaha domin ƙarfafa ilimin sana’a da kasuwanci.
You must be logged in to post a comment Login