Labarai
Za mu zamanantar da tashoshin mota – Muhammad Dig
Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta fara shirin gina sabbin wuraren ajiye motoci domin zamanantar da harkar sufuri a jihar.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin sufuri Alhaji Dalladi Idris Karfi ne ya bayyana hakan a madadin kwamishinan ma’aikatar sufuri Alhaji Mohammad Ibrahim Diggol a ziyarar da ya kai tashar Mota da ke Unguwa Uku.
Alhaji Dalladi Idris Karfi ya ce, an shirya ziyarar ne domin gano kalubale da matsalolin da ake fuskanta a bangaren sufuri.
A cewar sa, zamanantar da duk wasu tashohin moto a Kano zai bada dama wajen yin gogayya da sauran tashoshin kasashen da suka ci gaba a harkar sufuri.
Sai dai Alhaji Dalladi Idris Karfi ya bukaci ‘yan kungiyar ma’aikatan sufurin mota da su bada hadin kai wajen domin cimma burin da aka sa gaba.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar sufuri Ibrahim Adamu Kofar Nassarawa.
You must be logged in to post a comment Login