Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje : Za mu saka kafar wando daya da masu kin sanya Amawali

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata hada Kai da jamian tsaro domin shawo matsalar rashin sanya safar Baki da hanci da alumma basa dauka da muhimmaci.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a yau lokacin da yake gudanar da taron majalisar zartarwa da ake gudanarwar duk ranakun laraba aka kuma gudanar da shi a yau Talata.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kara da cewa hakika a nan Kano ana samun nasarar yakar Corona in akayi la’akari da yawan al’ummar da ake gwadawa wadanda ake samu da cutar basu da yawa adon haka ne ya yi kira ga al’umma wajen cigaba da  bin kaidojin yakar ta.

Ya Kara da cewa kasancewar har yanzu al’umma basu son sanya safar ta baki da hanci ba adon hakane ma ya ce zasu tattauna da jamian tsaro da sauran masu fada aji don ganin yadda zaa shawo kan alamarin.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce cigaba da fadakar da al’umma kan bin dokokin masana dongane da kariyar Corona zai taimaka wajen kawar da ita gaba daya.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!