Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

WAEC : Za’a bude makarantun boko a jihar Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta  ayyana ranar 10 ga wannan watan na Agusta a matsayin ranar da zata bude manyan makarantun sakadaren don  fara rubuta jarrabawar WAEC

Kwamishinan ilimi na jihar Dr, Shehu Makarfi ya sanar da hakan ta cikin sanarwar da ya fitar a yau Litinin cewa, umarnin ya yi dai-dai ne da umarnin da gwamnatin tarraya ta bayar na bude makarantu a ranar 4 ga wannan watan na Agusta.

A cewar Dr, Shehu Makarfi bude makarantu zai sanya dalibai  da za su kammala sakandire su rubuta jarrabawar WEAC ta bana.

Gwanan jihar Malam Nasir El-Rufa’I ne ya amince da bude makarantu a jihar ta Kaduna a ranar 10 ga watan Agusta wanda zai sanya su fara zaman rubuta jarrabawar a ranar 17 ga wannan wata na Agusta.

Akan haka ne ma’aikatar ilimi ta jihar ta umarci shugabanin makarantu su shirye don bude dalabai dake makarantun kwana makarantun kuma ‘yan aji uku na karshe don karbar su  yayin da za’a fara karatu gadan-gadan a ranar Litinin 17 ga wannan watan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!