Kimiyya
Za’a fara amfani da fasahar zamani don inganta noma- AATF
Shugaban kungiyar harkokin noma ta Afirka AAFT Dr Issuofou Kollo Abdourhamane ya ja hankalin kasashen Afirka wajen yin maraba da sabbin hanyoyin fasaha a matsayin wata hanya da za’a magance matsalolin karancin abinci da ke tunkarar nahiyar Afirka.
Dr Abdourhamane ya bayyana haka ne a yayin taron karawa juna sani na yan jaridu mai taken South west Agroecological ‘ da aka gudanar a jamiyar Obafemi Awolowo.
Ya ce wannan wani cigaba ne da ake samu ta hanyar fasaha, na samar da muhalli mai ingance ba tare da an gurbata shi ba.
Afirka zata iya samar da tsaftaccen abinci tare da magance matsala ta fari da yunwa da ka iya faruwa muddin ba’a samar da hanyar inganta samar da abinci ba.
Yana mai bayyana nau’ikan abincin da ka iya karanci a nahiyar Afirka sakamakon gurbatar yanayi ta hanyar wasu sinadaran da ke kashe albarkar kasa , ko magungunan kwari da wasu kamfanoni ke fitarwa ga muhalli.
A yanzu haka dai nahiyar Afirka musammam kasashen ke da sahara na gab da fuskantar rashin isasshen abinci.
Ya ce rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akalla kimanin fiye da yara miliyan 8 ne ke fama da yunwa , wanda adadinsu ya kai kimanin kaso 48 cikin dari dari na adadin lafiyayyun yara da ake da su a nahiyar Afirka a wannan karni.
Dr Issouffou ya ce amfani da fasaha ne kadai zai magance matsalolin da zasu magance fari da yunwa wanda kungiyar AATF ke aiki tukuru akan ta.
Ya kara da cewa tun da suka fara ayyuka a fannin cigaba na samar da abinci a Najeriya sun samar da ingantaccen irin rogo wanda ya taimakawa manoma samar da rogo na kimanin fiye da tan 32 a shekarun da suka gabata.
A yanzu haka suna kan aiki akan sarrafa noman shinkafa da inganta irin waken da kwari basa ci.
Da yake jawabi shugaban jami’ar ta Obafemi Owolowo farfesa Eyitope Ogungbenro Ogunbodede ya ce taron ya zo a lokacin da ake bukata, domin gwamnati na yunkurin tabbatar da abinci ya wadata a kasa baki daya
A hannu guda kuma gwamnati na kokarin samar da hanyar kudaden shiga.
Ya ce Najeriya na da adadin alumma da suka kai fiye da miliyan 170 , hakan ce ta sa samar da abinci ke da muhimmanci .
Ko a maganar da ake yi nan ba da jimawa ba gwmanatin tarayya tana dab da sayar da irin waken da kwari basa ci.