Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Daliban jami’ar KUST zasu fara zuwa Amurka don karo ilimi

Published

on

Jami’ar kimiyya da fasaha da ke Wudil da hadin gwiwar ofishin jakadancin Amurka a Najeriya zasu koyar da malaman jami’ar harkar gudanar bincike .

 

Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Alhaji Usman ne ya bayyana haka a yayin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin jakadancin Amurka a jami’ar a jiya.

 

Farfesa Musa wanda mataimakin sa Tijjani Sale Bichi ya wakilci shi ya ce sun shiga hadin gwiwar da ofishin jakdancin Amurka ne domin su horar da malamansu kan sanin makamar aiki tare da bunkasa harkokin ilimi a jihar Kano.

 

Mal Bichi dai farfesa ne a fannin kimiyya lissafi, ya ce jami’ar ta samu cigaba da dama a fannin inganta malamanta da bincike, ya kara da cewa hadin gwiwar ya zo a lokacin da ya dace.

 

Jamia’ar ta Wudil dai an kafa ta ne a shekara ta 2001 da tsangayu guda biyu dauke a dalibai guda 82, da malamai guda goma da sauran ma’aikata guda 14.

 

Ya yaba da ziyarar da ofishin jakadanci ya kai wa jami’ar, tare da cewar hadin gwiwar zai taimaka wajen inganta ta.

 

Da yake jawabi jami’ar ofishin jakadancin Amurka wanda shi ne ya wakilci tawagar Mr Sterlin Tilley zuwa jami’ar yace hadin gwiwar an yi sa ne domin inganta malamai tare da karfafa musu wajen gudanar da bincike.

 

Ya ce dalibai da jami’ar zasu sami damar ziyarta kasar Amurka domin bincike da karo ilimi.

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!