Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Sama da mutum 6000 ne suka mutu a Afirka

Published

on

Sabbin alkaluman da aka samu na masu dauke da cutar Covid-19 a Afirka ya nuna cewa kowacce kasa ta samu guzurin cutar a nahiyar, da ke da mutane sama da biliyan daya da digo biyu.

Ya zuwa ranar 13 ga watan Yuni, yawan wadanda suka mutu sanadin kamuwa da cutar Coronavirus a nahiyar ya haura 6000, ciki kuwa har da mutuwar tsohon shugaban Jamhuriyar Congo Jacques Joachim Yhombi-Opango da tsohon Firaministan Somalia Nur Hassan Hussein.

Yanzu haka dai akwai mutum 225,105 da aka tabbatar suna dauke da cutar Covid-19, inda 102,846 suka warke daga cutar, kamr yadda hukumar dakile yaduwar cutuka ta Afirka ta tabbatar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!