Labarai
za’a gyara gadar Muwo dake jihar Neja da ta rushe cikin kwanaki 3
Ministan ayyuka, samar da wutar lantarki da gidaje Babatunde Fashola, ya ce; za ayi gyara na wucin gadi a gadar mahadar titunan Mowo da ta hada garuruwan Mokwa da Jebba da ta rushe a baya-bayan nan cikin kwanaki uku.
Babatunde Fashola ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da wasu transfomomi a tashar tunkudo wutar lantarki da ke Zari’an jihar Kaduna.
Minista Babatunde Fashola, ya ce; a bangaren su, ba su da wani korafi kan rushewar gadar, saboda sun dauki lamarin a matsayin ikon Allah.
Ya ce, tuni ma’aikatar ta tura da kwararrun jami’anta wajen da lamarin ya faru domin daukar matakin gaggawa cikin awanni saba’in da biyu.
A jiya lahadi ne dai hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa FRSC, ta sanar da masu ababen hawa cewa, gadar mahadar titunan Mowo ta rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.