Kiwon Lafiya
Za’a hukunta wadanda ke da hannu a rikicin Filato
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya ce mutanen da aka kama kan zargin hannu cikin rikicin da ya wakana a Jihar kwanan nan da ya yi sanadyyar asarar rayuka da dukiyoyi, za su fuskanci Shari’a ne a garin Jos sabanin yadda aka saba gudanar da makamanciyar Shari’ar a birnin tarayya Abuja.
Lalong na bada wannan tabbaci ne lokacin da ya karbi wata kungiyar Kiristoci a fadarsa domin jajanta ma sa kan al’amarin da ke wakana a Jihar.
Gwamna Lalonga ya shaida wa kungiyar irin matakan da aka dauka na kawo karshen tashe-tashen hankula a Jihar, tare da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Jihar da ma kasa baki-daya.
Shugaban kungiyar Pentacostal Fellowship Rabaran Felix Omobunde ya tir da al’amuran da suka faru na kasha-kashe, sannan ya bukaci a kama duk masu hannu a ciki sannan a yi mu su Shari’a a Jihar ta Filato.