Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za’a kammala aikin shimfida layin dogo daga Legas zuwa badan kan Dala biliyan $ 1.6bn

Published

on

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce, za a kammala aikin titin jirgin kasa na Legas zuwa Ibadan wanda zai ci $ 1.6bn a watan Disambar bana ko kuma farkon Janairun sabuwar shekarar 2021.

Amaechi, ya bayyana hakan ne ya yin wani shirin talabijin kai tsaye daya gudanar a jiya Alhamis a birnin tarayya Abuja, da ya hada da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola.

Ya kuma ce zai yi aiki tare da Fashola da Gwamnatin Jihar Legas don kwashe manyan motocin daukar kaya daga kan tituna.

Da yake mayar da martani, Ministan Sufurin ya ce abin da takwaransa na ma’aikatar ayyuka da Gidaje ya bayyana dai-dai ne na hada gwiwa da Fashola da Jihar Legas don kara inganta harkar sufuri.

Amaechi ya ce a don haka za’a kammala aikin titin jirgin kasar a watan Disamba ko kuma farkon Janairun badi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!