Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za’a mangance matsalar ruwan sha a Sokoto

Published

on

Gwamnatin jihar Sokoto tare da hadin gwiwar Bankin duniya da gwamnatin tarayya sun bada aikin kwangila na samar da tsaftacen ruwan sha a waje da cikin kwaryar birnin jihar.

Mai rikon mukamin babban manajan a ma’aikatar ruwan sha na jihar Sama’ila Sanda ya bayyana hakan a ya yin bikin kaddamar da aikin.

Sama’ila Sanda ya bayyana cewar daga cikin ayyukan da za’a yi wajen samar da ruwan shan akwai sake gina madatsun ruwa da gina fanfon tuka-tuka a yankin Boda dake jihar ta Sokoto.

Ka zalika mai rikon mukamin babban manajan hukumar ya ce idan an kammala aikin samar da ruwan shan zai bunkasa ayyukan a’lummar yankin Bado da Kasarawa da ma sassa jihar baki daya.

Ya kuma shawarci dan kwangilar da ya kammala aikin akan lokaci da kuma aiki mai inganci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!