Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Asibitoci su dinga mika korafe-korafen su ga hukuma – Dr, Nasir Alhassan Kabo

Published

on

Darakta janar na hukumar dake kula da asibitocin jihar Kano Dr. Nasir Alhassan Kabo ya ja hankalin asibitoci da cibiyoyin lafiya dake sassan jihar nan da su zama masu mika koken su na duk wani abu da suke bukata ga hukumar akan lokaci.

Dr. Nasir Alhassan Kabo ya bayyana hakan ne yayin rabon kayan amfanin kananan yara da mata na wata-wata da hukumar ke gudanarwa.

Ya ce shakka babu kayan na taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar al’umma, wanda akan raba shi ga asibitoci da cibiyoyin lafiya dake karkashin hukumar.

Darakta janar na hukumar dake kula asibitocin na jihar Kano, ya kuma bukaci asibitocin da suka samu kayan a wannan lokaci da suyi amfani da su yadda ya dace.

Wakilin Umar Idris Shuaibu ya ruwaito cewa asibitoci hudu ne a wannan wata suka ci gajiyar kayan da Gwamnatin jihar Kano ke bayarwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!