Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fyade: Kotu ta zartarwa wani tsoho hukuncin “Rajamu”

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke ƙofar kudu a nan birnin Kano, ƙarƙashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin jefewa ga wani tsoho ɗan kimanin shekaru saba’in.

Kotun ta samu tsohon mazaunin garin Falsa dake ƙaramar hukumar tsanyawa da laifin yiwa yarinya ƴar shekara goma sha biyu fyade.

Kafin yanke hukuncin mai shari’a ya karantowa wanda ake tuhuma zargin, sannan aka bashi damar kare kansa, sai dai ya gaza kare kansa.

Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewa, hakane ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa bayan an haƙa rami tare da sanya gangar jikinsa a ciki.

Kotun ta baiwa wanda ake zargin damar ɗaukaka ƙara daga nan zuwa kwanaki talatin masu zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!