Labarai
Zabe : INEC ta tsaida ranar fara zaben cike gurabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tsayar da ranar 31 ga watan Oktobar bana, don gunadar da zaben cike gurbi na ‘yan majalisun tarayya a jihohi goma sha hudu na fadin kasar nan.
Zaben cike gurbin na sanatoci shida za a gudanar da su sakamakon mutuwar tsoffin sanatocin da kuma maye gurbin sanatan Bayelsa ta tsakiya Duoye Diri wanda ya zama gwamnan jihar.
Sanatocin da za a cike gurbin su, sun hada da sanata mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya da sanata mai wakiltar Arewacin jihar Cross River da Arewacin jihar Imo da kuma sanata mai wakiltar gabashin Legos sai kuma sanata mai wakiltar kudancin jihar Plateau.
Hakan na cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta INEC Festus Okoye ya sanyawa hannu mai dauke da kwanan watan 17 na Agustan da muke ciki a matsayin wa’adin kwnanakin da za a fara shirin gudanar da zaben cike gurbin.
Sanarwar ta kara da cewa, dukkanin jam’iyyun ‘yan takarar za su gudanar da zaben cikin gida don fitar da sunayen ‘yan takara tsakanin 24 ga watan Agustan da muke ciki zuwa 4 ga watan Satumba.
Okoye ta cikin sanarwar ya bayyana cewa dukkanin takardun cikewa na ‘yan takara za a dawo dashi hukumar ta INEC a ranar 9 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan.
You must be logged in to post a comment Login