Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalibai na fuskatar kalubalen rashin karafafa gwiwa – Kungiya

Published

on

Kungiyar daliban ‘yan aslin jihar Kano dake karatu a jami’ar addinin musulunci dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ta ce daliban ‘yan asalin jihar nan dake karatu  a can suna fuskantar kalubale ta bangaran rashin samun kwarin gwiwa daga nan gida.

Shugaban kungiyar Malam Dalha Sulaiman Ahmad ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radio wanda aka tattauana kan yadda dalibai ‘yan jihar nan dake gudanar da karatu a jihar maradi ke fuskantar matsaloli.

Ya kara da cewar duk da cewar kyauta suke gudanar da karatun a jami’ar kamata yayi daga nan gida Kano su samun goyan baya ta kowane bangare wajan kyautata karatun nasu.

Shugaban ya kuma ce ana gudanar da karatu a jami’ar kamar yadda ake gudanarwa a sauran jami’o’i a jihar nan sai yanayin yadda ake kashe kudi wajan samun gurbin karatu ne ya ban-banta.

Ana ta bangaran shugabar kungiyar da bangaran mata Khadija Sulaiman Tudun Murlata ta bayyana basa samun matsala rashin jituwa tsakanin dalibai mata da kuma malamai kamar yadda ake samu a wasu jami’o’in kasar nan.

Khadija Sulaiman kuma ta yi kira ga iyaye musamma ma mata wanda basu da dabi’ar barin yaran su karatu a wasu jami’o’i dasu basu dama shiga jami’ar addinin musulunci dake Maradi duba da cewar ta ban-banta da sauran jami’o’in kasar a wajen bada tarbiyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!