Labarai
Zaben Amurka zai haifar da ci gaba a dimokuradiyya – Abbati Bako
Cibiyar nazarin dimukuradiyya da shugabanci ta ce sakamakon zaben kasar Amurka zai haifar da ci gaba da dama musamman ta fannin dimokuradiyya.
Shugaban kungiyar Dakta Abbati Bako ne ya bayyana hakan ta cikin shirin barka da hantsi na nan tashar freedom wanda ya mayar da hankali kan yadda zaben amurkan da ya gudana.
Ya ce kin daukar matakin gaggawa kan cutar Covid-19 da Donal Trump ya yi ya taka rawa matuka wajen faduwar sa zabe.
Dakta Abbati ya kara da cewa sabon shugaban kasar Amuruka Joe Biden zai iya farfado da sassan tattalin arzikin kasashen da suka durkushe a sakamakon cutar corona da kuma sauran kasashe masu tasowa.
A yau ne dai ake sa ran sabon shugaban Amuruka Joe Biden zai kaddamar da kwamitin masana mai kunshe da mutane goma sha biyu wadanda zasu tallafa wajan kawo karshen annobar corona.
You must be logged in to post a comment Login