Connect with us

Labarai

Zaɓen shugabannin mazaɓu na APC ba zai hana mu tsaftar muhalli ba – Dr. Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, zaɓen shugabannin mazaɓu na jam’iyyar APC a matakai daban-daban da za a gudanar ba zai hana yin aikin tsaftar muhalli na ƙarshen wata ba.

 

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, jim kaɗan bayan kammala duban tsaftar muhalli na ƙarshen wata da aka gudanar a wasu ma’aikatun gwamnati a Juma’ar nan.

 

Getso ya ce, kamar kowacce Asabar ɗin ƙarshen wata ma’aikatar muhalli za ta gudanar da duban tsaftar muhalli a faɗin jihar Kano.

 

A Asabar ɗin nan ne dai za a gudanar da zaɓen shugabannin mazaɓu na jam’iyyar APC anan Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!