Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Zafin Kishi : Uwargida ta bankawa gidan Amarya wuta a Kano

Published

on

Ana zargin wata uwargidan da bankawa gidan kishiyarta wuta da yammcin jiya Lahadi a yankin Liman Gwazaye dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Shaidun gani da Ido sun bayyana wa Freedom Rediyo cewa, matar da ake zargin ta fito ne daga gidan bayan anfara neman daukin kashe gobarar Daga makota.

A cewar su amaryar taje unguwa ne kafin faruwar lamarin da yammacin ranar Lahadi.

Shima Mai Gidan Malam Iliyasu Abdullahi Umar, ya bayyana cewar lokacin da zai tafi kasuwa ya bar mukullin gidan a gurin Uwargin sa, kasancewar Ya kai amaryar domin taga gida bayan watanni uku da Aurensu.

Da wakilin mu ya zanta da Amaryar da ake zargin gidan nata ya kone tace akwai bukatar mata su rage kishi kasancewar tana zargin kishiyar tata ce ta kunna mata wutar wacce tayi sanadiyar konewar kayan dakinta baki daya sai kujeru biyu da suka rage kawai.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa, da ya yi kokarin jin tabakin wacce ake zargin amma hakan ya faskara sakamakon Awon gaba da ‘Yansanda suka yi da Ita don gudanar da bincike.

Sai dai da wakilin mu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘Yansandan Kano DSP Abdullahi Haruna, ta wayar tarho bai sami sukunin daga wayar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!