Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana zargin Miji da shanye jinin al’adar matar sa a Kano

Published

on

Kotun shari’ar musulunci mai lamba daya karkashin jagorancin mai sharia Abdullahi Halliru Kofar Na’isa ta fara sauraron shari’ar da wata mata ta shigar gabanta tana rokon kotun ta datse igiyar auren ta da mijinta.

Matar ta bayyana wa kotun cewar, maigidan nata yana yi mata surkulle har ta kai jallin yana ritsa ta da wuka akan lallai sai ta bashi dama ya shanye jinin al’adar ta domin ya biya bukatarsa.

Sai dai mijin matar da ake zargi da aikata wannan laifi yace kalan sharri ne kawai matar tasa tayi masa.

Daga bisani dai kotun ta sanya ranar ashirin da hutu ga watan gobe domin cigaba da sauraron shaidu .

Barrista Abdurrashid Balarabe Adam Dandago shine lauyan wadda ta shigar da kara ya kuma ya yi karin haske akan da’awar da suka yi a gaban Kotun a zamanta Kotun na yau.

Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya yi kokarin jin tabakin mijin matar amma abin ya faskara.

Sai dai  maigidan nata  ya yi kurin cewa, idan a aka zo kotun a ranar 24 ga watan gobe domin za mu ga abin mamaki a wannan rana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!