Labarai
Zamfara: Yan sanda sun tabbatar da sace mutane uku a harin da yan bindiga suka kai

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da sace mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi a daren ranar Laraba a kauyen Tsauni da ke karamar hukumar Gusau.
Mai magana da yawun rundunar, ya ce an baza jami’an tsaro a yankin domin kubutar da mutanen tare da kamo wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.
Haka kuma ya ce, wadanda aka sace din sun hada da Kansiloli biyu da kuma wani limamin yankin.
Rahotonni sun bayyana cewa, wannan harin ya kara jefa al’ummar yankin cikin tsoro da fargaba, kasancewar ya na daga cikin hare-haren da suka saba faruwa a jihar.
You must be logged in to post a comment Login