Labarai
Zamu ƙara ƙarfafa Alaƙa tsakanin Jami’an tsaro da Ƴan Jarida
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ƙara inganta alaƙar aiki tsakanin jami’an tsaron ƙasar nan da ma’aikatan yaɗa labarai domin samar da ingantaccen aiki da tabbatar da yaɗa labaran gaskiya a faɗin jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya
Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano Baba Halilu Ɗan tiye ne yayi wannan jawabin yayin da yake gabatar da lakca ga hafsoshin sojojin ƙasar nan da suka zo jihar domin gudanar da binciken karatu kan alakar aiki tsakanin jami’an tsaro da rundunar tsaro ta ƙasa
A dan haka gwamnatin Kano ta ce wannan bincike da hafsoshin tsaron ƙasar nan suke yi abi ne da zai ƙara samar da alaƙar aiki tsakanin su da sauran jami’an ƙasar nan, ganin yadda suka zagaya dukkan nin Shalkwatar hukumomin tsaro dake jihar Kano da sauran guraren tarihi na jihar domin jin yadda tarihin Kano yake da irin dabi’un mutanen Kano
Baba Halilu Ɗan tiye ya kuma ce kasancewar wani lokacin akan sami saɓani tsakanin tsakanin ƴan jarida da jami’an tsaro ya sanya gwamnati zata ƙara inganta alaƙar aiki tsakanin su
Da yake jawabi sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bayyana farin cikin sa yayi kan yadda suka kawo masa ziyara da yadda suka zaɓi jihar kano a matsayin inda zasu gudanar da binciken su
Da yake jawabi shugaban hukumar ƴan sanda na jihar Kano CP Muhammad Ussaini Gumel cewa yayi kasancewar yadda ake samin yawaitar aikata laifuka ya zama wajibi ƴan sanda da sojoji su haɗa kai domin samar da tsaro a faɗin ƙasar nan
Haka abin yake ga shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kano Abubakar Idris Ahmad cewa yayi dama ya kamata irin wannan manyan jami’an na ƙasar nan da su dunga zuwa hukumomin tsaro domin ganin yadda suke gudanar da aikin su
A ƙalla sama da hafsoshin tsaron ƙasar nan talatin da biyar ne suka zo daga makarantar koyon sanin makamar aiki ta rundunar tsaro ta ƙasa dake garin jaji dake jihar Kaduna domin gudanar da bincike da dabi’un al’ummar jihar Kano kasancewar mafi yawa daga cikin hafsoshin tsaron ba ƴan arewa ba ne
You must be logged in to post a comment Login