Labarai
Zamu ci gaba da zamanantar da kasuwar Rimi -Shugaban kwamiti
Kwamitin tsara kasuwar Rimi da zamanantar da ita ya ce karamar hukumar birnin Kano za ta ci gaba da zamanantar da kasuwar Rimi kamar yadda sauran kasuwannin suke, duk da irin korafe-korafen da wasu ‘yan kasuwar ke yi kan wannan aiki.
Shugaban kwamitin tsara kasuwar Rimi da zamanantar da ita Abdulhamid Sarki Bababa ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a harabar kasuwar dake birnin Kano.
Abdulhamid Sarki ya kara da cewa sun dauki lokaci mai tsaho suna gudanar da gyararraki a kasuwannin cikin birnin Kano domin zamanantar da su cikin kwanciyar hankali sai dai a wannan karo sun samu tsaiko a wani bagare na kasuwar Rimi wanda hakan ya sanya aka dakatar da aikin.
Gwamnatin Kano ba ta tallafawa kasuwar Rimi -Shugaban kasuwar
Akwai bukatar samar da kasuwar mata zalla a Kano
An bukaci ‘yan kasuwa da su sabunta lasisinsu
Ya kara da cewa karamar hukumar birnin Kano za ta ci gaba da gudanar da ayyukan gyaran kasuwannin cikin birnin Kano domin mayar da ita ta zamanu gaba daya.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito shugaban kwamitin na cewa wadanda suke korafi da aikin da karamar hukumar ke yi dama can ba ainihin wajensu bane sun zauna a wajen ne zaman wucin gadi kuma zasu ci gaba da gudanar da aiki a kasuwar domin ciyar da kasuwar Rimi gaba.
You must be logged in to post a comment Login