Labarai
Zamu dauki mataki akan jami’anmu dake hada kai da ‘yan siyasa -Hukumar kula da shige da fice
Zamu dauki mataki akan jami’anmu dake hada kai da ‘yan siyasa -Hukumar kula da shige da fice
Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa, Muhammad Babandede ya ce hukumar su a shirye take domin daukar tsatsauran mataki akan duk wani jami’in ta da ta kama da laifin kulla alaka da wani dan’ siyasa ko mai hannu da shuni wajen karya dokar Hukumar.
Muhammad Babandede ya Kara da cewa sun sami labarin cewa Yanzu jami’an su basa bincikin yan’siyasa ko musu hannu da shuni a lokacin da suke kokarin ketaro iyakar kasar nan.
Muhammad babandede ya bayyana hakan ne lokacin da ake Karin girma ga masu taimakawa Kwantrola janar guda goma sha hudu da akayi jiya A birnin tarayya Abuja.
Haka kuma yace kimanin Mutane Goma Sha biyar Ne Hukumar zata hukunta bisa zarginsu da mabambanta laifuka.
Muhammad Babandede ya kuma shawarci sababbin masu taimaka masa dasu sanya ido Akan jami’ansu domin yin aiki kamar yanda yake.
A cewar sa ya zuwa Yanzu akwai masu hannu da shuni da yan’siyasa da suke tunanin zasu yi yin komai da kansu, batare da zuwa offishin hukumar hana fasa kauri ba.
A don haka yake kira da babbar murya kancewa duk wanda suka kama da irin wannan laifin ba shaka zasu dauki mataki akan sa.
LABARAI MASU ALAKA:
Hukumar hana fasa kwauri ta kama wasu motocin alfarma 18
An kawo gawar jami’in hukumar fasakwauri Nura Shu’ibu Kano