Labaran Kano
Zamu Faɗaɗa Kasuwar Wambai da Zamanantar da Ita
Shugaban kasuwar ƙofar Wambai Alhaji Nasihu Ahmad Garba (Wali Ɗan China) ya ce zai bi duk wata hanya wajen ganin ya zamanantar da harkar kasuwancin kasuwar wambai da kuma haɓɓaka shi domin ciyar da jihar Kano gaba a fagen kasuwanci
Wali Ɗan China ya kuma ce zasu yi duba da irin halin da kasuwar take ciki na cushewa wajen ganin sun samar da hanyoyi domin yin zirga-zirga cikin sauki a cikin kasuwar musamman yadda motoci zasu dunga shiga ko wanne lungu domin kai kaya da kuma bayar da taimakon gaggawa
Haka kuma zamu fito da ofishin shugabancin kasuwa domin ƴan kasuwa su san menene manufar ofishin, kasancewar a baya ba’a san anfanin ofishin ba illa kawai ƙungiyoyin ƴan kasuwa, to dole yanzu haka wannan ofishin ya samar da wani tsari da zai haɗa kan ƙungiyoyin ƴan kasuwan
Wali Ɗan China Ya kuma ce, zasu nemi su sami wata kyakkyawar alaƙa tsakanin su da hukumar KAROTA, wajen rage takurawa ƴan kasuwar wambai musamman yadda a kullum suke samin barazana tsakanin su da hukumar sakamakon yadda suke kama musu kaya da zarar sun fito zasu kai wani waje
Ɗan China ya ce zasu ƙara ƙarfafa harkar kasuwancin su wajen wayar wa da ƴan kasuwar kai domin zuwa ƙasashen waje don kulla alaƙa da su, domin yin kasuwanci da kuma kasuwancin zamani
Ina kira ga ƴan kasuwar wambai da su fito su haɗa kai domin ganin an ciyar da kasuwarcin kasuwar wambai gaba
You must be logged in to post a comment Login