Labarai
Zamu fito da tsarin rage shan mai ga injinan haskaka wutar lantarki a Kano-Abdullahi Garba Ramat
Shugaban hukumar kula da hasken wutar lantarki na kan titina da kawata burni na jihar Kano, ya bayyana cewa sun fito da tsarin rage shan mai ga injinan da suke bada hasken wutar lantarki a wani mataki na kara inganta tattalin arzikin jihar Kano.
Injiniya Abdullahi Garba Ramat ne ya bayyana hakn jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan tashar freedom radio da ya mayar da hankali kan matsalolin rarraba hasken wutar lantarki a jihar Kano.
Ya ce, a baya jihar Kano na bukatar mega wart 8 na hasken wutar lantarki sai dai a yanzu sun fito da tsarin amfani da mega wart 2 yana mai cewa hakan shi ne zai nuna ana tafiya da ci gaban zamani.
Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya kara da cewa, duk wani sabbin tsare- tsaren samar da hasken a kan titinan jihar nan ana sa ran za a kammala shi nan da watanni uku masu zuwa in da kuma hukumar ta fito da tsarin samar da cibiyar da zata rinka nunawa masu ababen hawa yanayin yadda cinkoson titina yake a danjoji.
Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya bukaci al’ummar jihar Kano da su basu goyon baya wajen yin amfani da duk wani abu na ci gaba da gwamnati ta samar wanda hakan ne zai taimaka wajen inganta ayyuakan ta.
You must be logged in to post a comment Login