Connect with us

Labaran Kano

Samar da lantarki mai amfani da hasken rana ne kadai zai magance tashin gobara a kasuwanni

Published

on

Shugaban kasuwar Muhammad Abubakar Rimi wato sabon gari  dake Kano Alha Uba Zubairu Yakasai ya ce amfani da lantarki na haske rana ce kadai hanyar da zata magance matsalar gobara da ake yawan samu wanda ke haddasa asara da dama.

 

Alh Zubairu ya bayyana haka ne  yayin da yake zantawa da manema labarai da aka gudanar  yau a offishin kungiyar yan jaridu dake kano.

 

Ya jaddada cewar sanya lantarki mai amfani da hasken rana ce kadai zai magance matsalolin da yan kasuwa ke fuskanta musammam ma matsaloli da suka shafi yawan tashin gobora da ake samu wanda ke haddasa asarar dukiyoyi da dama.

 

Ya ce tsarin samar da lantarki mai amfani da hasken rana na daga cikin tsare-tsaren da gwamatin tarayya ta fito da shi a wasu daga cikin kasuwannin da ke fadin kasar.

 

Ya bukaci ‘yan kasuwa da su marawa gwamnatin tarayya baya dangane da wannan yunkuri nata na samar da lantarki mai amfani da hasken rana don magance matsala ta gobora.

 

Alh Zubairu ya bukaci shugabannin da ke aikin samar da wutar lantarkin ta hanyar amfani da hasken rana da su rage farashin da suke shirin bayarwa domin saukakawa ‘yan kasuwa.

 

A cewar sa samar da wutar lantarki da wani kamfani ke ba su  wanda ake yi wa lakabi da merger na daga cikin dalilan da ya sa wasu ‘yan kasuwa suka ki karbar lantarki mai amfani da hasken rana

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,603 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!