Labaran Kano
Zamu gina Asibitoci a sabbin masarautu 4 na Kano- Ganduje
Gwamnatin jihar Kano tace tuni ta bayarda kwangilar gina Asibitoci a dukkannin sabbin masarautin jihar Kano hudu wadanda zasuci gadaje dari hudu domin bunkasa harkar lafiya a jihar Kano.
Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya bayyana hakan a yayin taron Kungiyar Likitocin kananan yara ta kasa NAPCON.
Alhaji Usman Alhaji yace banda gwamnatin jihar Kano babu wata jiha a fadin Najeria data warewa bangaren lafiya kaso mafi yawa acikin kasafin kudinta sai jihar Kano.
Sakataren gwamnatin jihar Kano Usman Alhaji ya kuma nanata cewa gwamnatin jihar Kano zata cigaba da bunkasa harkar lafiya domin ciyarda bangaren lafiya gaba.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa Sakataren gwamnatin Kano Usman Alhaji na cewa gwamnatin Kano zata cigaba da baiwa bangarorin ilimi da lafiya fifiko sama da komai kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta shaida cewa duk kasar dake son cigaba dole ne sai ta fifita wadannan bangarori guda biyu