Labaran Kano
Zamu hada kai da manyan makarantu don bada horon aikin Gona-KSADP
Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano, Kano State Agro Pastoral Project KSADP, zai tallafawa dalibai 100 na jiha masu shaidar karatun Difiloma ta kasa (Diploma) da babbar Difiloma (HND), wajen basu horo na musamman akan Noma da kiwo da sauran aiyyukan Gona.
Shugaban shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano Malam Ibrahim Garba , ya bayyana haka a yau lokacin da ya ke karbar tawagar jami’an Kwalejin aiyyukan gona ta tarayya wato Federal College of Agricultural Produce, a ofishin sa.
Malam Ibrahim Garba , ya ce horon za a bada shi ne a Kwalejojin aiyyukan gona dake jiha.
Labarai masu Alaka.
Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi
Shirin Bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano zai fara Bayen Shanu
“Abune mai muhimmanci mu koyar da ma’aikatan gona ilimin aikin don gudanar da aikin yadda ya kamata tare da samar da wadataccen Abinci ga al’ummar kasar nan, don haka zamu hada kai da makarantar ku da ire -iren su don samar da horon ga daliban”.
” Shirin zai taimaka wajen bayar da horo na musamman ga ‘yan kasuwar Dawanau masu siyar da Gari na kayan Abinci don tabbatar da ingancin sa zuwa kasashen Ketare don haka muna bukatar taimakon ku wajen bada horo ga dalibai”.
A nasa jawabin shugaban makarantar Muhammad Hadi Ibrahim wanda ya samu wakilcin Sakataren bangaren koyar wa wato ‘Academic’, Sirajo Salisu ya ce “Makarantar tana da rawar da zata taka don haka ta shigo cikin shirin gadan -gadan don bunkasa harkokin noma a fadin jiha da kasa baki daya.
A sanarwar da kakakin shirin Aminu Kabir Yassar, ya rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun sa, ta ruwaito shugaban makarantar na cewa, Kwalejin tana da izinin bada horo ga manoma ,tare da samar da kuma killace kayan da aka noma don adana su ba tare da sun lalace ba.
” Kwalejin mu tana bada horo ga manoma , kungiyoyi, ‘yan kasuwa ,matasa da kuma kungiyoyin mata akan yadda zasu yi aiyyukan su tare da Adana su , don tabbatar da sun samu sana’oin dogara da kan su ” inji Sirajo Salisu.
You must be logged in to post a comment Login