Labarai
Zamu inganta harka noma a kasar nan-AFAN
Gamayyar kungiyoyin manoma AFAN a Nijeriya ta ce zata inganta rayuwar manoma ta hanyar samar mus tallafi da kuma taki ciki sauki.
Shugaban Kungiyar Dakta Farouk Rabi’u Mudi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da Freedom radiyo.
Dakta Farouk ya Kuma ce ‘manoma na Cikin wani hali biyo bayan tsadar taki zamani da ake fuskanta wanda hakan ke jawo tsadar kayan abinci’.
Ya kuma ce ‘sun dauki matakai dama wajen ganin sun gujewa faruwa ambaliya ruwa’.
Inda kuma yayi kira ga gwamnatin tarraya data samu ta yashe dam dam din da ake dashi a fadin kasar nan domin gujewa ambaliya ruwa.
Haka zalika ya ce ‘manoma da su guji yin shuka a wuraren dake da tarihin ambaliyar ruwa’.
You must be logged in to post a comment Login