Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu sa a cafke Ɗanzago idan ya kuma cewa shi ne Shugaban Jam’iyya – APC Gandujiyya

Published

on

Jam’iyyar APC tsagin Gwamna Ganduje ta ce, za ta sanya jami’an tsaro su cafke Ɗanzago, idan ya ƙara bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyya.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

Aruwa ya ce, Ɗanzago sojan gona yake yiwa shugabancin jam’iyyar, tunda ba shi da shaidar zama shugaba.

Ya ƙara da cewa, ya zama dole su ɗauki mataki matuƙar Ɗan Zagon ya sake bayyana kansa a matsayin shugaba.

A ranar Asabar ne Ɗanzago ya sake jaddada matsayarsa inda ya ce, shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!