Labarai
Zamu saka idanu domin ganin an tafiyar da sabuwar dokar zabe a Najeriya – CISLAC
Ƙungiyar CISLAC mai sa ido kan ayyukan majalisun dokokin Najeriya ta ce za ta saka idanu domin ganin an tafiyar da sabuwar dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu.
A yau Juma’a 25 ga watan Fabrairun 2022 shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanyawa dokar hannu.
Shugaban kungiyar Kwamred Auwal Musa Rabsan Jani, kuma jami’in kungiyar Transparency International mai yaƙi da cin hanci da rashawa, a Najeriya ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Freedom Radio.
Auwal Musa Rabsan Jani ya ce “ Sanyawa dokar hannu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi zai rage cin hannu da rashawar dake damun kasar nan”.
Ya kuma ce “ yiwa dokar zabe karan tsaye da wasu daga cikin shugabannin Najeriya ke yi zai kau daga lokacin da dokar ta fara aiki”.
Auwal Musa Rabsan Jani ya kuma godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kokarin da ya yi na sanyawa dokar hannu duk kuwa da cewa wasu daga cikin ‘yan siyasar Najeriya basu so hakan ba.
You must be logged in to post a comment Login