Labarai
Zamu tallafawa manoma da irin shuka a jihohi goma sha uku-INCRISAT
Gwamnatin tarayya ta ce zata raba ingantaccen irin shuka da kayan noma ga kananan manoma sama da miliyan biyu a kasar nan don inganta harkokin nona musamman a Daminar bana.
Ministan Noma Alhaji Sabo Na-Nono ne ya bayyana hakan a yayin da yake kaddamar da bayar da iri kyauta ga kananan manoma da suka fito daga jihohin kasar nan goma sha uku da wata cibiya mai bincike kan shuke-shuke da irin Noma wato (INCRISAT) ta samar don rabawa manoma, wanda suka hadar da irin Dawa da Gero da Wake da kuma Shinkafa don tinkarar damunar bana.
Sabo na Nono ya kuma ce gwamnatin tarayya ta shirya baiwa manoman kasar nan kayan aiki da tallafin bashi ga manoman da zasu gudanar da noma a damunar bana.
Nan bada jimawa za’a fara fitar da shinkafa zuwa ketare -Nanono
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta fitar da tan dubu 70 na abinci don tallafawa mabukata-Nanono
Da yake jawabi shugaban cibiyar ta (INCRISAT) Dakta Hakeem Ageibe, ya ce zasu raba tallafin ne ga kananan manoma sama da dubu takwas don aikin noman bana.
Ya kuma ce, duba da wannan lokaci da ake cikin na annobar Corona ya sanya da yawa daga cikin kananan manoman kasar nan sun cinye amfanin gonar tasu da zasu sake shukawa a gonakin su wanda hakan ya sanya zasu basu tallafin irin shukar.
Hakeem ya ce irin da zasu rabawa manoman na musamman ne da zai iya fitowa a gonakin su cikin kankanin lokaci, ba tare da daukan lokaci mai tsawoba.
Ya yin ziyarar Mininstan Noman Sabo na Nono, ya shawarci manoman da zasu amfana da tallafin shukar da suyi amfani da shi ta yadda ya kamata wajen bin shawarwarin masana kan yadda zasu amfani abin da suka shuka din.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa Cibiyar ta (INCRESAT) ta bukaci manoma da su dan jinkirta fara shuka a wannan lokaci da damuna bata gama kankama ba, kasancewar hakan ka iya lalata musu shukar ta su.
You must be logged in to post a comment Login