Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Barka Da Hantsi

Masu ɗauke da cutar sukari na cikin haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki – Dakta Kamalu

Published

on

Wani ƙwararren likitan masu fama da cutar sikari a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce, masu fama da cutar sikari na cikin haɗarin fuskantar shanyewar barin jiki.

Dakta Kamalu Sidi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan freedom radiyo wanda ya mayar da hankali kan ranar masu fama da ciwon sikari da aka gudanar a jiya.

Dakta Kamalu Sidi ya ce, ba iya manya ne kaɗai ke kamuwa da cutar sikari ba, domin kuwa a yanzu har da ƙananan yara.

Har ma ya ce “masu shan taba sigari da barasa suna cikin barzanar kamuwa da cutar sikari sakamakon sinadaran da suke sanyawa jikin su”.

“Ana iya gadon cutar sikari, yayin da a gefe guda wasu abubuwan da mutane ke ci na taka rawa wajen samar da ciwon sikari a jikin su musamman masu zaƙi da maiƙo kuma ba tare da mutuum in ya ci yana motsa jiki ba”.

Dakta Kamalu ya kuma ce “shan lemukan gwangwani da na roba da na kwali na iya haddasa cutar sukari su ma, sannan yawan fita fitsari musamman a cikin dare da kuma saurin gajiya da zarar mutum yayi tafi na cikin alamomin cutar” a cewar likita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!