Labarai
Zan ci gaba da kare kaina a gaban kotu – Abduljabbar
Malamin nan Abduljabbar Kabara ya bayyanawa kotu cewa zai ci gaba da kare kansa a gabanta.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kotun ta ce lauyoyinsa sun miƙa mata takardar ficewa daga daga shari’ar.
Ko da kotu ta tambayi Abduljabbar ɗin kan ficewar lauyoyinsa daga shari’ar sai ya ce “Ina da masaniyar hakan hasalima ni ne na koresu sakamakon sun saɓa yarjejeniyar da muka ƙulla“.
Dan haka Malamin yace shi yanzu a kyaleshi zai ci gaba da kare kansa anan ne mai gabatar da ƙara ya tashi yace ai a ƙa’ida ba za’a ci gaba da shari’ar ba tare da Lauya ba.
A yau ne dai aka ci gaba da sauraran shari’ar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar Kano da Malam Abduljabbar Kabara a babbar kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a kofar kudu ƙarƙashin jagorancin mai Sharia Ibrahim Sarki Yola.
Inda Lauya mai gabatar da ƙara Farfesa Nasir Adamu Aliyu ya jagoranci sauran lauyoyin.
Daga ƙarshe kotum ta ce a rubuta takarda zuwa ga hukumar dake kula da lauyoyi don su bai wa Abduljabbar ɗin Lauyan da zai kareshi kamar yadda wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito.
You must be logged in to post a comment Login