Connect with us

Siyasa

Zan mara baya ga duk wanda ADC ta tsayar takarar shugaban kasa – Atiku

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC baya a zaɓen 2027, yana mai cewa haɗin kai ne zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi.

Hakan na zuwa ne bayan INEC ta dakatar da hulɗa da shugabannin ADC tare da cewa ba za ta sa ido kan babban taron jam’iyyar da ake shirin yi ba, matakin da jam’iyyar ta yi watsi da shi tana mai cewa za ta ci gaba da shirinta.

Atiku ya kuma jaddada cewa jam’iyyar na bai wa matasa da mata muhimmanci, yana danganta matsalolin tsaro da na tattalin arziki a ƙasar da rashin aikin yi da ƙarancin ilimi, yana mai cewa ’yan Najeriya na neman sauyi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!