Labaran Kano
Zan yiwa karamar hukumar Dala aikin Naira miliyan 500 – Yakudima
Danmajalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala Babangida Abdullahi Yakudima yace zai kawo aiki na Naira miliyan dari biyar a mazabar Dala.
Babangida Abdullahi Yakudima ya bayyana haka ne lokacin shirin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyan Freedom.
Yace a ayyukan da danmajalisa yake yiwa al’umma ya yayi tanadi mai kyau ga al’ummar karamar hukumar ta Dala wajen horar da matasa da bayar da jari.
Bayan haka ya dauki kwararru da zasu zo da tsare tsare masu kyau wajen ganin an samarwa al’ummar ta karamar hukumar Dala mafita a harkokin yau da kullum.
Babangida Yakudima yace a kasafin kudin shekarar 2021 kuwa zai gudanar da ayyukan da suka kai Naira biliyan daya a mazabar ta Dala.