Connect with us

Labarai

Zanga-zanga ta barke a Rano bisa zargin yan sanda da hallaka wani matashi

Published

on

Wani rikici ya barke a karamar hukumar Rano ta jihar Kano a yau Litinin biyo bayan mutuwar wani matashi mai suna Abdullahi Musa inda rahotonni suka ce ya mutu a hannun ‘yan sanda yayin da ake yi masa tambayoyi.

 

jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, an kama Abdullahi ne a ranar Lahadin da ta gabata kan wani laifin da ake zarginsa da aikatawa, mutuwar tasa ta haifar da bacin rai, wanda ya janyo barkwar zanga-zanga musamman ma tsakanin matasamman yankin.

 

Da farko dai lamarin ya fara ne da zanga-zangar lumana kafin daga baya ta rikide zuwa tashin hankali yayin da masu zanga-zangar suka mamaye ofishin yan sanda na na garin tare da kone shi a matsayin martani ko kuma daukar fansa.

 

A yayin hargitsin, rahotonni sun bayyana cewa wani dan sanda ya samu rauni bayan da masu zanga-zangar suka kai musu hari.

 

Jami’in wanda ba a bayyana sunan sa ba, an ce ya na karbar magani a wani wurin jinya da ba a bayyana ba.

 

Shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya kara ta’azzara ne a lokacin da ake zargin ‘yan sanda sun bude wuta don tarwatsa taron zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkata wasu matasa biyu.

 

Haka kuma jaridar ta kara da cewa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar mata da faruwar lamarin inda ya ce, za a gudanar da cikakken bincike kan ainahin abinda ya faru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!