Labarai
Zanga-zanga: Za mu kawo karshen yajin aikin ASUU – Gwamna Ganduje
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta sanar da shirinta na yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ASUU.
Cikin shirin nata, da dauki gabarar bada shawarwari ga bangarorin biyu wato gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU.
Gwamna Kano Dakata Abdullahi Umar Gandije shi ne yayi wannan jawabi lokacin da tawagar masu zanga-zangar lumana ta yada zango a gidan gwamnatin.
A cewar Ganduje “mu gamayyar gwamnonin Najeriya za mu tunkari gwamnatin tarayya da shawarwari domin ganin dalibai sun koma karatun su”.
“Mun sani rashin biyan malamai albashi babbar matsala ce ga bangaren ilimi, don haka muna nan muna shiri don kawo karshen wadannan matsaloli” in ji Ganduje.
Wakilyar Freedom Radio Zahrau Nasir ta ruwaito cewa kungiyoyi daban daban ne suka halarci zanga-zangar lumanar wadda kungiyar kwadago ta shirya.
You must be logged in to post a comment Login