Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin ɓatanci: Kotu ta aike da Ɗan Sarauniya gidan gyaran hali

Published

on

Kotun majistire mai lamba 58 ƙarƙashin mai shari’a Aminu Gabari ta aike da tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Ma’azu Magaji Ɗan Sarauniya zuwa gidan gyaran hali.

An aike da Ɗan Sauraniya gidan gyaran halin ne bayan da kotun ta fara sauraron shari’ar a ranar Litinin wadda ƴan sanda suka shigar.

Ƙarar wadda aka yi zargin Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan sarauniya na yunƙurin ɓatawa gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje suna sakamakon wallafa wani hoto da yayi a shafin sa na Facebook.

Tun da fari dai wani lauya ne mai suma Adekunle Taiwo ne ya shigar da ƙara a madadin gwamnan Kano kan wancan zargi wanda ya kira a matsayin cin mutunci ga gwamnan.

Yayin da ake karanta masa tuhumar Ɗan Sarauniya ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen, sai da
Lauyan mai ƙara Wada A. Wada ya roƙi kotun da ta sanya wata ranar dan su gabatar da shaida.

Barista Garzali Datti Ahmad shi ne Lauyan wanda ake tuhuma shi ma ya roƙi kotun da ta sanya Ɗan sarauniyar a hannun beli inda ya ɗora hujja da sashi na 35 dana 36 (5) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Ya kuma tallafi roƙon da sashi na 168 da na 172 da kuma sashi na 172 na kundin tafikar da Shari,ar ACJL 2019.

Har ma Barists Garzali Datti Ahmad ya bayyana cewar Ɗan sarauniyar bashi da ƙoshin lafiya kuma idan har aka bada belinsa ba zai tsere ba, ba kuma zai kawo tarnaki a binciken ƴan sanda ba.

Nan ne mai gabatar da ƙara Wada A. Wada yayi suka inda ya bayyana cewar batun rashin lafiya da lauyan kariya yayi batu ne mara tushe saboda babu wasu gamsassun takardu da suka tabbatar da cewar wanda ake tuhumar bashi da lafiya.

Ya kuma roƙi kotun da ta yi watsi da roƙon lauyan kariya, wanda a nan ne kotun ta aike da Ɗan Sarauniya zuwa gidan gyaran hali kamar yadda wakilin Freedom Radio Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!