Labarai
Zargin badakala: majalisar dattijai ta bukaci ministar kudi ta gurfana a gabanta
Majalisar dattijan kasar nan ta bukaci ministar kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad da Akanta na tarayya Ahmad Idris da su gurfana gabanta, kan zargin fitar da kudi kimanin sama da naira biliyan bakwai daga asusun hukumar bunkasa fasahar motoci da ke karkashin bankin Najeriya.
Kwamitin majalisar da ke sanya idanu kan Kudaden Jama’a ne ya bukaci da su gurbafana a gaban sa.
Kwamitin yayi zargin cewa an fitar da kudi na farko da yawan su ya kai sama da naira biliyan uku sai kudi na biyu da aka fitar shima da ya kai sama da naira biliyan biyu a shekarar 2005 da kuma wata biliyan daya da aka fitar a shekarar 2006.
A cewar rahoton babban Akanta Janar na tarayya wanda kwamitin majalisar dattawa ke nazarta karkashin jagorancin Sanata Matthew Urhoghide, ya bayyana cewa an cire kudaden ne tsakanin watan Maris da Disambar shekarar 2000.
A cewar kwamitin, lokacin da ya tuhumi darakta janar na hukumar Jelani Aliyu ga me da fitar da kudin, sai yace an cire su ba tare da sanin hukumar ba.
You must be logged in to post a comment Login