Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin cire ido: Ƴan sanda sun gurfanar da dattijuwa a gaban kotu

Published

on

Ƴan sanda sun gurfanar da dattijuwar nan Furaira Abubakar Isah a gaban kotu da matashin da ake zargi Isah Hassan.

Ana dai zargi dattijuwa Furaira mazaunoyar garin Ɗan tsinke a ƙaramar hukumar Tarauni da laifin ƙwaƙulewa wani yaro ido don yin tsafi.

An gurfanar da ita a gaban kotun majistire mai lamba 12 a ranar Laraba sakamakon zarginsu da hada kai wajen yunƙurin kisan kai ta hanyar cirewa wani karamin yaro idanu.

Yayin zaman kotun mai gabatar da kara lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soron Ɗinki ya roƙi kotu data bada dama a karantowa waɗanda ake tuhuma laifin su.

Kotun ta amince ƙarƙashin jagorancin Muhammad Jibril, jami’in kotun jikan Dabo ya kuma karanto zargin.

Jim kaɗan bayan fitowa daga kotun Freedom Radiyo ta zanta da dattijuwar mai kimanin shekaru 117 Furaira Abubakar inda ta ce “Yaron sharri yayi mun ba ni na saka shi ba, ba ni da lafiya ma, amma yaron yayiwa wanda aka cire idon kwatancena don na bashi magani shi ne ya biyo ni da sharri”.

Shi ma matashin mai shekaru 17 Isah Hassan bayan ya ce “Jikanta ne ya haɗa Ni da ita za ta bani maganin tsari tun da ina shiga daji inyo gawaye, sai ta ce sai na samo idanun mutum amma yana wahala idan za a yi kayar ɓata”.

Ya ci gaba da cewa “Sai ta ce dubu ɗari 2 ma ba za ta isa ka sayi ido ba amma zan baka wani magani, kuma da ta bani maganin gaba daya kai na ya juya”.

Sai dai lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soron Ɗinki, jim kaɗan bayan fitowa daga kotun ya ce duba da cewa kotun bata da hurumin saurarar shari’ar yasa suka kara rubuta takardar tuhuma zuwa babbar kotun jiha.

Daga karshe mai shari’a Justice Muhammad Jibril, ya dage shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Afrilu domin ci gaba da saurarar ta, inda kuma nan take ya bayar da umarnin ci gaba da tsare mutanan da ake zargi.

Hakan yasa jami’an gidan ajiya da gyaran hali da suka hadar da ASC Yahaya Mustafa da Inspector Muhammad Ahmad da Alasan Ya’u suka tafi dasu domin tsare su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!