Labaran Kano
Zargin dura ashar ya janyowa malamin Jami’a zaman gidan yari anan Kano.
Kotun majistret mai zamanta a Rijiyar zaki ta aike da wani malamin jami,a gidan gyaran hali bisa zargin bata suna da cin mutunci.
Tun da farko yansanda ne suka gurfanar da wannan lakcara mai suna mustafa Hashim Kurfi wanda wani mai suna Abba musa yayi korafi akan sa.
Kunshin tuhumar ya bayyana cewar Abban yayi korafin cewar lakcaran ya duddura masa ashariya da shi da ‘’yan uwansa ta wayar tarho harma Abban ya nadi muryar malamin yana ta runtuma ashar koda yake malam Mustafa Hashim kurfi ya musanta zargin .
Barrister Ma’aruf Muhammad Yakasai shine lauyan da yake kare Mustafa Hashim ya kuma roki kotun da ta sanya shi a hannun beli kasancewar akwai dangantakar auratayya tsakanin mai kara da wanda ake kara.
Sai dai mai gabatar da kara Yusuf Saleh yayi suka inda yace da zarar an bayar da belin Mustafan zai haifar da tarnaki ga binciken ‘Yansanda.
Mai Sharia Aminu usman Fagge ya sanya ranar 19 ga wannan watan dan bayyana matsayar kotun ya kuma yi umarnin a tsare malamin zuwa waccan rana.