Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Majalisar ta bukaci gwamnati ta gina makarantun firamare a karamar hukumar Ungogo

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Kano da ta gina Sababbin makarantun firamare a wasu unguwanni da garuruwa guda goma sha daya da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudrin da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo Aminu Sa’ad Ungogo ya gabatar yayin zaman majalisar da ya gudana a ranar lititin.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar, Aminu Sa’ad Ungogo, ya ce, sakamnakon Karin yawan jama’a a yankin ya sanya su ke da  bukatar karin makarantun firamare, Wanda ya ce hakan zai taimaka wajen kaddamar da shirin ba da ilimi  kyauta da gwarmnatin Kano ta kaddamar a wannan shekara.

Yankunan da ke bukatar sababbin makarantun firamare sun hada da Sharifai-kadage da Bachirawa Yamma da Tudun Rubudi da Rumawa da Zaura Kadage de Kuma Rijiyar Zaki-Arewa. Sauran sune Zangen Kaya da Karon Buzaye da Gandar da Unguwarafa da Kuma Daurawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!