Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Zargin Yin Barazana: Ƴan sanda sun gayyaci Malam Abduljabbar

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gayyaci Malam Abduljabbar Kabara, kan ƙorafin da shugaban Izala na jihar Dr. Abdullahi Saleh Pakistan yayi a kansa.

Da maraicen Asabar ɗin nan, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa Freedom Radio cewa, an gayyaci malamin don ya bayyana a ranar Litinin mai zuwa.

A cewar sa, dama an ɗage wannan gayyatar ne, saboda zaman muƙabalar da aka yi da shi a ranar Asabar.

Tun a baya ne shugaban ƙungiyar Izalar Dr. Abdullahi Pakistan, ya shigar da ƙorafi gaban rundunar ƴan sandan, kan zargin Malam Abduljabbar da yin wasu kalamai da ke yi masa barazana ga rayuwa.

Wanda ƴan sanda suka ce, sun shiga bincike tun a kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!